Accessibility links

Shugaba Mohammed Morsi Ya Tsaya kan Bakarsa


Shugaba mohammed Morsi yana jawabi ta telebijin ga al'ummar Misra ran alhamis 6 Disamba, 2012

Shugaban yace ba zai yarda da kashe-kashe ko makarkashiya ba, ya kuma ce ‘yan daba karnukan farautar wasu su na ta kitsa haddasa fitina a kasar.

Shugaba Mohammed Morsi na Misra, yace ba zai yarda da kashe-kashe ko makarkashiya ba, ya kuma ce ‘yan daba karnukan farautar wasu su na ta kitsa haddasa fitina a kasar. Shugaba Morsi yayi magana ne jiya alhamis ta telebijin na kasar a yayin da zanga-zangar nuna kin-jinin gwamnati ke kara kamari a al-Qahira.

Shugaba Morsi ya bayyana takaicin mutanen da aka kashe da wadanda suka ji rauni a wannan tashin hankali, yayin da ya dage cewa tattaunawa ce kawai zata kai ga warware rikicin tsarin mulki na kasar.

Yace an kashe mutane 7 a tashin hankali cikin dare a kofar fadar shugaba, yayin da wasu fiye da 700 suka ji rauni. Yace an kama mutane 80 a saboda aikata laifuffuka ciki harda amfani da bindigogi, har ma ya bayyana wasu daga cikin wadanda aka kama a zaman mutanen da aka biya kudi domin su tayar da fitina.

Har ila yau shugaban ya bayyana cewa daga gobe asabar za a kaddamar da abinda ya kira “cikakkiyar tattaunawa mai ma’ana da amfani” da shugabannin ‘yan hamayya, da nufin kaucewa karin tashin hankali kafin kuri’ar raba-gardamar da za a jefa kan sabon tsarin mulki a ranar 15 ga watan nan na Disamba. Ba a san ko shugabannin hamayyar zasu halarci wannan tattaunawa ba.

Shugaba Barack Obama na Amurka yayi magana da shugaba Morsi ta wayar tarho jiya alhamis domin bayyana damuwa kan mace-mace da raunuka a lokacin zanga-zangar. Wata sanarwar fadar White House ta kuma ce Mr. Obama yayi kira ga dukkan shugabannin siyasa na Masar da su bayyanawa magoya bayansu a fili cewa ba za a yi na’am da tayar da hankali ba.
XS
SM
MD
LG