Accessibility links

Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Falasdinu


Falasdinawa su na bukukuwan murna bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da Falasdinu a zaman kasa 'yar kallo

Wakilai 138 suka yarda da kara matsayin Falasdinawa a majalisar, yayain da kasashe 9 kawai suka jefa kuri'ar kin yarda, wasu 41 kuma suka kaurace

Da gagarumin rinjaye, Babban Zauren taron Majalisar Dinkin Duniya, ya jefa kuri’ar amincewa da kasar Falasdinu wadda za a ba ta matsayin ‘yar kallon da ba cikakkiyar wakiliya ba a majalisar.

An barke da sowar murna a zauren majalisar ta dinkin duniya jiya alhamis a bayan da aka amince da wannan kuduri da kuri’u 138 na goyon baya, da kuri’u 9 na rashin goyon baya, yayin da kasashe 41 suka kauracewa jefa kuri’a. A bayan da aka jefa kuri’ar ta amincewa da kasar Falasdinu, su ma Falasdinawa a garin Ramallah, dake yankin yammacin Kogin Jordan, sun bingire da nuna farin ciki ka’in da na’in, su na sumbatar juna tare da matsa hon na motocinsu.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, yace wannan kuri’a da aka jefa ta jaddada irin bukatar gaggawa dake akwai ta komawa ga tattaunawa mai ma’ana a tsakanin Isra’ila da Falasdinawa. Yayi kira ga dukkan sassan da su sake jaddada kudurinsu na cimma zaman lafiya ta hanyar tattaunawa.

Amma jakadiyar Amurka a Majalisar, Susan Rice, ta bayyana wannan kuri’a a zaman ta “takaici wadda kuma zata haifar da kishiyar abinda ake nema,” tana mai fadin cewa ta gindaya wasu shingaye ga cimma zaman lafiya. Rice ta ce Amurka zata bukaci dukkan sassan da su guji daukan karin matakan tsokanar juna, su kuma koma ga yin shawarwari nan take ba tare da gindaya wata ka’ida ba.

Wannan karin matsayi da martabar diflomasiyya da Babban dakin Shawara na MDD ya ba Falasdinawa, zai kyale majalisar mulkin kan Falasdinu ta samu shiga cikin wasu muhimman hukumomi da cibiyoyi na majalisar, kamar kotun bin kadin manyan laifuffuka ta duniya.
XS
SM
MD
LG