Accessibility links

Shugaba Obama Ya Lashi Takobin Yin Amfani Da Duk Ikonsa


Shugaba Barack Obama yana magana a wajen zaman makoki a Newtown, Connecticut 16 Disamba 2012.

Domin tabbatar da cewa bala’i irin na kashe yara kanana 20 da wasu manya 6 ranar jumma’a a wata makarantar firamare ta Amurka bai sake faruwa ba.

Shugaba Barack Obama na Amurka ya lashi takobin yin amfani da duk ikon da yake da shi domin tabbatar da cewa bala’i irin na kashe yara kanana 20 da wasu manya 6 ranar jumma’a a wata makarantar firamare bai sake faruwa ba.

Daren lahadin nan shugaba Obama ya shiga sahun masu jimami a garin Newtown na Jihar Connecticut, inda wani saurayi ya harbe mutanen su 26. Shugaban yace ba su kadai suke jimami ba, al’umma a fadin Amurka baki daya su na taya su bakin cikin wannan abu.

Mr. Obama yace wannan kisan gilla ya haddasa ayar tambaya a zukatan Amurkawa. Ya lura cewa wannan shi ne karo na hudu da ake aikata irin wannan kisan kiyashi tun sadda ya fara mulki shekaru hudu da suka shige.

Shugaban na Amurka ya ce, "Wannan abu ya ishe mu haka. Tilas ne mu kawo karshen irin wannan bala’i, amma tilas mu canja halayenmu in muna son kawo karshensa. Za a yi ta fada mana cewa ai dalilan irin abu su na da sarkakiya. Gaskiya ne cewa babu wata doka ko jerin dokoki da zasu iya kawar da mugunta ko tayar da hankali a kasa. Amma kuma, wannan ba dalili ne na nade hannu da kasa yin komai ba."

Tun da fari, shugaban ya gana da iyalan wadanda aka kashe musu ‘ya’ya ko ‘yan’uwa a makarantar firamare ta Sandy Hook dake garin na Newtown, ya kuma godewa wadanda suka fara kai dauki wurin.
XS
SM
MD
LG