Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Indiye Ya Fadi Yadda Aka Yi Ma Abokiyarsa Fyade


Wani dattijo a Indiya yana kunna kyandir a wurin tunawa da dalibar da ta mutu bayan an yi mata fyade a New Delhi, a kasar Indiya

Wannan hira ta gidan telebijin na Zee TV ita ce karon farko da wannan saurayi ya fito yayai magana a kan abubuwan da suka faru ranar 16 Disamba

Abokin wata matashiya mai shekaru 23 da haihuwa ‘yar kasar Indiya wadda ta mutu makon jiya a saboda raunukan da ta samu a lokacin da aka yi mata mummunan fyade cikin wata motar bas a New Delhi, ya fito a karon farko ya fada ma wani gidan telebijin na Indiya abubuwan da suka faru.

Wannan saurayi ya fada jiya jumma’a cewa sai da aka dauki mintoci 25 kafin wani ya tsaya ya taimake su a bayan da aka jeho su gefen hanya, tsirara, daga cikin motar.

Yace a lokacin da ‘yan sanda suka iso, sun tsaya su na ta musu da junansu a kan ko wanene yake da iko a kan wannan batun tsakaninsu.

Wannan hira da aka yi a gidan telebijin na Zee TV shi ne karon farko da wannan saurayin da ba a fadi sunansa ba, yayi magana a bainar jama’a kan harin da aka kai musu shi da wannan daliba ranar 16 ga watan Disamba.

Yace a cikin motar ‘yan sanda, ba wai a cikin motar daukar marasa lafiya ba, aka dauke shi da ita zuwa asibiti inda yace ya zauna tsirara na tsawon awoyi da yawa a kasa ba tare da an zo an duba shi ba.

Wannan daliba ta mutu ranar asabar da ta shige a wani asibitin kasar Singapore, inda aka kai ta jinya.

Hukumomin Indiya sun gurfanar da mutane 5 gaban kotu su na tuhumarsu da kisan kai, fyade, satar mutum da wasu laifuffukan. Hukumomi sun ce zasu nemi da a yanke hukumcin kisa a kansu idan an same su da laifi. Mutum na shida an ce shekarunsa bai kai 18 ba, saboda haka za a gurfanar da shi a gaban kotun yara.

Fyade da mutuwar wannan daliba sun haddasa zanga-zanga da nuna bacin rai a duk fadin kasar Indiya.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG