Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Seleka Sun Sake Kwace Wani Garin


Sojojin gwamnati su na sintiri a kan titi a birnin Bangui, 1 Janairu 2013.
Sojojin gwamnati su na sintiri a kan titi a birnin Bangui, 1 Janairu 2013.

Gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da mazauna garin Alindao dake kusa da Bambari, sun ce a yanzu haka 'yan tawaye ke rike da garin Alindao.

Rahotanni daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun ce wata gamayyar ‘yan tawaye ta sake kwace wani garin, ‘yan kwanaki kadan kafin ta fara tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar.

Rahotanni daga gwamnati da kuma mazauna garin Alindao, dake kusa da garin Bambari, sun ce wannan gari (Alindao) ya shiga hannun ‘yan tawaye. Kamfanin dillancin labaran AP ya ambaci wani mazaunin garin yana cewa an kwace shi daga hannun gwamnati. Idan har aka tabbatar da wannan labari, to zai zamo na baya bayan nan a cikin garuruwa da kauyukan da ‘yan tawaye suka kwace cikin wata gudan da ya shige.

Sabbin rahotannin su na janyo ayar tambaya a kan yiwuwar tattaunawar neman zaman lafiya da aka shirya farawa jibi talata a Libreville a kasar Gabon.

A ranar Jumma’a, Kwamitin Sulhun MDD yayi kira ga ‘yan tawayen da suka dirkaki babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da su dakatar da wannan farmaki nasu, su shiga cikin tattaunawa da nufin samo madafar siyasa ta warware matsalolin wannan kasa mai fama da talauci.

Gamayyar ‘yan tawaye ta Seleka ta kunshi kungiyoyin ‘yan tawaye har hudu daga yankin arewacin kasar wadanda suka ce gwamnati ta ki cika alkawuran da ta yi karkashin yarjejeniyoyin zaman lafiya na 2007 da 2008 wadanda a karkashinsu aka ce za a biya ‘yan tawaye kudi domin su ajiye makamansu, ko kuma a shigar da su cikin rundunar sojojin kasar.

Gamayyar ta Seleka ta ce tilas shugaba Francois Bozize ya sauka daga kan mulki.
Mr. Bozize yace a shirye yake ya kafa gwamnatin hadin kan kasa, amma yana da niyyar kammala wa’adinsa na biyu kan karagar mulki wanda ba zai cika ba sai a shekarar 2016.
XS
SM
MD
LG