Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Isra'ila Sun Fatattaki Falasdinawa

Mazaunar Isra'ilawa kennan dake Maaleh Adumim. Dec. 2. 2012

Runudnar ‘yan sandan Isra’ila tayi amfani da karfi wajen korar Falasdinawan dake zanga-zanga a yankin Falasdinawan da Isra’ila ta mamaye yanzu take kokarin gigginawa Yahudawan kama wuri zauna gidaje a Yammacin Kogin Jordan.

‘Yan kishin kasar Falasdinu sun kokarta kakkafa tantuna a yankunan nasu da ake kira da lakabin E-1 ran Juma’a, suka ce suna karfafa cewar yin haka ne zai sa Isra’ila ta tsaida gine-ginen da take yi yanzu a Yammacin Kogin Jordan.

Falasdinawa sun yi watsi da gargadin da sojin Isra’ila suka yi masu na su janye, don haka yau lahadi safe sai ‘yan sandan Isra’ila cikin motocin rusa gine-gine suka bulla a yankin inda suka rika bi suna rurrusa tantunan ‘yan falasdinu.

Yahudawan kama wuri zauna a Isra’ila sun jima dama suna shiga yankunan Falasdinawa suna giggina gidaje tare da ikrarin ai yankin na daga cikin wuraren da Isra’ila ta mamaye a Yammacin Kogin Jordan.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG