Accessibility links

Kungiyar Al-Shabab Ta Yanke Shawarar Kashe Dan Faransa


Hoton dan Faransa kennan wanda ake kira Dennis Allex a hoton da shafin al-Shabab ya wallafa ran Yuli 9 2010
Kungiyar ‘yan gwagwarmayar Somaliya al-Shabab tace ta shirya daukan matakin kashe dan Faransa da suke garkuwa da shi ‘yan kwanaki kadan bayan kokarin da Faransa tayi na kokarin ceto shi amma bata sami nasara ba. Bayan ta kasa cin nasara sai Faransa ta dauka mutumin ya mutu.

A wata sanarwa ranar Laraba ‘yan gwagwamayar sun ce sun cimma shawarar baki daya su kashe dan leken asirin Faransa Denis Allex.

Ana tsare Allex tun lokacin da aka sace shi daga birnin Mogadishu daga wani otel a watan Yuli a shekarar 2009. Kafin lokacin yana cikin ayarin dake horar da dakarun gwamnatin Somali domin yakar al-Shabab.

Dakarun Faransa sun yi kokarin kubutar da Allex a wani samame da suka kai ranar Juma’a lamarin da yayi sanadiyar mutuwar sojojin Faransa biyu da mayakan al-Shabab 17

Al-Shabab tace fararen hula dakarun Faransa suka kashe lokacin samamen. Kungiyar tace zata kashe Allex domin daukan fansar wadanda suka mutu kuma ta nuna rashin amincewarta da abun da ta kira manufofin Faransa da suka nuna kin jinin Islama da kuma shigar da dakarun Faransa suka yi cikin Afghanistan da Mali.
XS
SM
MD
LG