Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hillary Clinton Ta Bayyana Damuwa Kan Ci Gaba Da Garkuwa Da Mutane A Aljeriya


Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, a lokacin da ta ke magana kan batun garkuwa da mutane a Aljeriya, Jumma'a 18 Janairu, 2013
Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, a lokacin da ta ke magana kan batun garkuwa da mutane a Aljeriya, Jumma'a 18 Janairu, 2013

Kafofin labarai na Aljeriya sun ce an kashe mutane akalla 12 a wannan lamari na garkuwa da mutane da ake ci gaba da yi a yankin hamadar kasar.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ce ta damu matuka game da lamarin nan na garkuwa da mutane da ake ci gaba da yi a kasar Aljeriya, ta kuma yi kira ga gwamnatin Aljeriya da ta dauki dukkan matakan da zata iya domin ceton rayuka.

Clinton ta bayyana wannan a taron ‘yan jarida na hadin guiwa da tayi da sabon ministan harkokin wajen Japan jiya jumma’a a Washington, yayin da kafofin yada labarai na gwamnatin Aljeriya suke fadin cewa mutane akalla 12, ‘yan Aljeriya da ‘yan kasashen waje, sun mutu, a bayan farmakin da sojojin gwamnatin Aljeriya suka kai.

Da maraicen jumma'a, jami’an Amurka sun tabbatar da cewa akwai Ba Amurke guda daya a cikin wadanda suka mutu.

Clinton ta bayyana halin da ake ciki a zaman mawuyaci kuma mai hatsari, amma kuma ta ce ba zata yi karin bayani ba a saboda dalilan tsaro. Har ila yau ta ce yana da matukar muhimmanci ga Amurka ta fadada tare da karfafa yunkurin yaki da ta’addanci na hadin guiwa da Aljeriya da dukkan kasashen dake yankin.

Tun fari a jiya din, kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Aljeriya yace an kwato ‘yan kasashen waje su kusan 100 wadanda masu kishin Islama suka kama suka yi garkuwa da su ranar laraba, yayin da har yanzu ba a san halin da wasu fiye da 30 suke ciki ba.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG