Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barack Obama Ya Fara Wa'adi Na Biyu Kan Mulki


Babban jojin Amurka, John Roberts, yana rantsar da Shugaba Barack Obama a Fadar White House, Lahadi 20 Janairu, 2013.

Duk da cewa yau litinin za a sake rantsar da shugaban a bainar jama'a, Obama yayi rantsuwar fara aiki kamar yadda tsarin mulki yace a ran 20 Janairu.

A hukumance, shugaba Barack Obama na Amurka yayi rantsuwar fara wa'adi na biyu kan karagar mulki a wani bukin da shi da iyalansa suka halarta a fadar White House.

Jiya lahadi Mr. Obama yayi rantsuwar a yayin da ya dora hannunsa kan wani Baibul na iyalan maidakinsa, Michelle Obama.

Tun da fari a jiya lahadin, shugaba Obama da mataimakinsa Joe Biden, wanda aka riga aka rantsar a jiyan, sun fita zuwa Makabartar Gwarzayen Kasa ta Arlington, inda kamar yadda aka saba suka ajiye furanni a jikin dogonyaro na tunawa da sojojin da suka mutu a bakin daga.

Tsarin mulkin Amurka ya tanadi cewa lallai a rantsar da shugaban kasa a ranar 20 ga watan Janairu. Da yake ranar ta fado a kan ranar da aka saba hutu ne wato lahadi, shugaban da mataimakinsa zasu sake yin rantsuwa a wurin bukin rantsar da shugaban kasa da aka saba yi bisa al'ada a bainar jama'a yau litinin a kofar Majalisar Dokoki.

Yawan jama'a da zasu taru don bukin rantsarwar da za a yi yau litinin, ba zai kai na rantsar da shugaba Obama da aka yi na farko ba, inda mutane kusan miliyan biyu suka makare farfajiyar ginin majalisa da filin shakatawa na kasa dake gabanta domin kallon abin tarihi na rantsar da shugaban kasa bakar fata na farko.

A yau, mutane kimanin dubu 800 ne aka yi kiyasin zasu halarci bukin rantsar da shugaban na biyu kuma na karshe.
XS
SM
MD
LG