Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Duniya Su na Ci Gaba Da Taya Barack Obama Murna


Shugaba Barack Obama lokacin da yake jawabin nasara daren talata a Chicago.

Sakonnin taya murna na ci gaba da kwarara a bayanda shugaban ya doke Mitt Romney na jam'iyyar Republican a zaben shugaban Amurka na ran talata

Shugabannin kasashen duniya su na ci gaba da aika sakonnin taya murna ga shugaba Barack Obama na Amurka, wanda ya lashe zaben wa'adi na biyu a bayan da ya doke Mitt Romney na jam'iyyar Republican.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, yace ya taya Mr. Obama murna sosai, kuma yana sa ran ci gaba da yin aiki tare da shi karkashin inuwar kawance mai dorewa dake tsakanin Amurka da majalisar.

Firayim minista David Cameron na Britaniya yace yana sa ran ci gaba da hada kai da Mr. Obama. Yace munanan abubuwan da suke faruwa a kasar Sham sun nuna a fili irin bukatar dake akwai ga Britaniya da Amurka su zage damtse wajen warware wannan rikici.

Shugaba Francois Hollande na Faransa ya fadawa Mr. Obama cewa sake zabensa da aka yi, zabe ne a fili na goyon bayan "budaddiya, hadaddiyar Amurka mai taka rawa sosai" a harkokin duniya.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar China ta ce shugaba Hu Jintao da mutumin da zai gaje shi nan ba da jimawa ba, mataimakin shugaba Xi Jinping, su na sa ido ga yin aiki tare da Mr. Obama.

Firayim minista Benjamin Netanyahu na Isra'ila yace babban kawancen dake tsakanin Amurka da Isra'ila yana da karfi fiye da kowane lokaci, kuma zai ci gaba da yin aiki tare da shugaba Obama. Shi dai Mr. Netanyahu, dadadden aboki ne na Mr. Romney, dan takarar jam'iyyar Republican da ya sha kaye a zaben talata.
XS
SM
MD
LG