Accessibility links

An kashe mutane biyar a Kano ran talata, yayin da aka harbe wasu 18 cikin kasuwar garin damboa dake Jihar Borno da maraicen litinin

Wasu mutanen da ake kyautata zaton masu kishin Islama ne sun hallaka mutane 23 a wasu hare-hare biyu dabam-dabam a yankin arewacin Najeriya.

A hari mafi muni, wasu ‘yan bindiga sun bude wuta a wata kasuwa a Jihar Borno, suka kashe mutane 18 da maraicen litinin. Wani masarauci a yankin mai suna Abba Ahmed, yace an kai harin ne a garin Damboa dake Jihar ta Borno.

Babu wani tabbas game da musabbabin kai wannan harin, amma mutanen garin na Damboa sun ce watakila an kai harin ne a kan mafarauta na garin dake sayar da irin naman nan da ake kira “Bush Meat” da turanci, wanda ya hada da naman birai, wanda musulmi a yankin ke kyama.

A wani lamarin dabam da ya faru jiya talata kuma, wasu ’yan bindiga a kan babura sun harbe suka kashe mutane 5 dake wasan dara a birnin Kano. Mutane biyu sun ji mummunan rauni a harin.

Hukumomi sun yi imanin cewa ‘ya’yan kungiyar nan ta Boko Haram ne suka kai hare-haren guda biyu.

Kungiyar ta kashe daruruwan mutane a cikin shekarar da ta shige a kyamfe da take yi na neman ganin an kafa tsarin shari’a mai tsauri a yankin arewacin Najeriya.

Hukumomi a Jihar ta Kano dai, sun hana daukar fasinja a kan babura daga ranar alhamis 24 ga watan Janairu.
XS
SM
MD
LG