Accessibility links

Za'a Tsaurara Wa Korea ta Arewa Takunkumai


Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kennan a lokacin da suke ganawa akan Korea ta Arewa. Junairu, 22 2013. (AP Photo/Mary Altaffer)
Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bada umarnin a tsaurara takunkumin karya tattalin arziki kan Korea ta Arewa saboda harba roka da ta yi cikin watan Disemba, mataki da ya sa Korea ta Arewa ta kangare har da nuna alamun cewa zata ma yi gwajin nukiliya.

Wakilan kwamitin su goma sha biyar baki dayansu jiya talata suka kada kuri’ar yin Allah wadai da harba kumbon, suna masu cewa ai gwajin makami mai linzami ne da aka haramta mata a karkashin kudurorin Majalisar Dinkin Duniya kan kasar da suke aiki yanzu.

Haka kuma kwamitin ya yi barazanar daukan karin “matakai masu tsanani”, idan Korea ta Arewa ta kaddamar da wani gwajin.

Nan da nan kuwa Korea ta Arewa ta maida martani, cewa ba zata sake shiga shawarwari da nufin kawarda dukkan harkokin nukiliya a zirin koriya ba. Daga nan ta yi alwashin zata habaka matakan soji da nukiliyarta a matsayin kariya, kalaman da wasu suka fassara a matsayin barzanar gwajin makamin nukiliya.

A lokutan baya, har sau biyu, Korea ta Arewan ta yi gwajin makaman nukiliya bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabata mata takunkumi bayan ta harba kumbo zuwa sararin subahana. Hotuna da taurarin dan adam suka dauka a baya-bayan nan sun nuna cewa kasar tana shirin yin gwaji na uku.
XS
SM
MD
LG