Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Kafa Sansani, Watakila A Nijar


Jirgin leken asiri wanda ba ya da matuki cikinsa, samfurin RQ-4 Global Hawk

Amurka tana shirin kafa sansanin jiragen da ake sarrafa su daga kasa a Arewa maso yammacin Afirka, domin karfafa ayyukan leken asiri a kan kungiyoyin ‘yan kishin Islama a yankin.

Rahotanni daga kafofin labarai, sun ce Amurka tana shirin kafa sansanin jiragen da ake sarrafa su daga kasa a yankin Arewa maso yammacin Afirka, domin karfafa ayyukan leken asiri a kan kungiyoyin ‘yan kishin Islama a yankin.

Rahotanni sun ambaci wasu jami’an gwamnatin Amurka wadanda suka bukaci da kada a bayyana sunayensu, su na fadin cewa watakila za a kafa wannan sansani ne a Jamhuriyar Nijar.

Suka ce idan har akia amince da wannan shiri, sansanin zai iya kunsar sojojin Amurka guda 300.

Nijar tana makwabtaka da kasar Mali inda sojojin Faransa da na Mali suke gwabzawa da masu kishin Islama.

Jaridar “New York Times” wadda tafara ba da wannan rahoto, ta ambaci wani jami’in sojan Amurka, yana cewa babban makasudin sansanin shi ne rikicin da ake yi a Mali, amma kuma sansanin zai yi amfani ga ayyukan leken asiri na Amurka a fadin yankin baki dayansa.

Amurka tana da sansanin soja kwaya daya ne tak na dindindin a nahiyar Afirka, wanda ke kasar Djibouti, mai tazarar kilomita dubu 5 daga kasar Mali.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG