Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Jarida Uku Sun Shiga Hannu A Kano


Hoton masu aikin yin allurar cutar shan inna su na shirin fara yiwa yara rigakafi a Kano, Najeriya

'Yan sanda sun kama 'yan jarida uku na gidan rediyon Wazobia dangane da kisan da aka yiwa masu aikin yin allurar rigakafin cutar shan inna a Kano

‘Yan sanda a arewacin Nageria sun kama ‘yan jarida uku da aka alakanta da kisan masu aikin yin allurar cutar shan inna tara a makon jiya a wani asibiti.

‘Yan jaridar wadanda ke aiki a gidan rediyon Wazobia FM ana zargin su ne da yin zugar da ta janyo kashe-kashen a cikin wata tattaunawar da su ka yi a rediyo kan shaci fadi da kuma jamhurun da ake yayatawa game da shirin rigakafin cutar shan inna.

Shugaban gidan rediyon, Sanusi Bello Kankarofi, ya ce da yammacin lahadi aka bukaci ‘yan jaridar uku su amsa kira a wani ofishin ‘yan sanda, kuma kwamishinan ‘yan sandan jahar Kano Ibrahim Idris ya tabbatar da kama su.

Ranar jumma’a wasu ‘yan bindiga a kan babura su ka kashe masu aikin yin allurar shan innar su tara, dukan su mata, sun rutsa su ne a lokacin da su ke kan aikin su na yin allurar cutar shan inna a wasu asibitoci biyu a cikin birnin Kano.

Babu tabbas game da wadanda su ka harbe ma’aikatan, amma an sha dora alhakin kai irin wadannan hare-hare kan kungiyar Boko Haram ta masu kishin Islama.

Wasu ‘yan arewacin Najeriya sun yi amanna cewa ana yin amfani da allurar polio ne don a hana mata haihuwa ko kuma ta na iya haddasa kamuwa da kwayar cutar kanjamau.

Najeriya na cikin kasashen duniya uku inda har yanzu ake samun cutar polio. A bara kasar ta bayar da rahoton samun yara dari da ishirin da daya da suka kamu da cutar, wanda shi ne adadin sabbin kamuwan da ya fi na ko'ina yawa a duniya.

wata yarinya mai suna Niima Ahmed wadda polio ta gurgunta a Kano
wata yarinya mai suna Niima Ahmed wadda polio ta gurgunta a Kano

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG