Accessibility links

Jirgin Ruwan Da Ya Makale Da Mutum Dubu 4 Ya Komo Tasha


Ana jan jirgin ruwan fasinja na Carnival Triumph zuwa cikin tashar ruwan Mobile, Alabama, daren Alhamis 14 Fabrairu, 2013.

Jirgin ruwan fasinja mai suna "Carnival Triumph" yayi kwanaki tsaye a tsakiyar teku bayan da injunan wutar lantarkinsa suka lalace.

Wani jirgin ruwan yawon shakatawa na kamfanin Carnival da ya lalace ba wuta ba hanyar yin amfani da wuraren bahaya, a tsakiyar teku dauke da dubban faisnjoji, ya samu kaiwa cikin tashar jiragen Mobile a Jihar Alabama.

Wasu kananan jiragen ruwan jan jirage sune suka janyo wannan jirgi dauke da fasinjojinsa, ya kuma shiga cikin tashar cikin daren nan na alhamis.

Rahotannin sun ce fasinjojin dake cikin jirgin ruwan, wadanda suka yi kwanaki su na korafin kazanta da kuma dogon layin karbar abinci a cikin jirgin, watakila zasu shafe awoyi da dama kafin su iya sauka.

Akwai mutane fiye da dubu 4 cikin wannan jirgi na kamfanin Carnival mai suna Carnival Triumph, a lokacin da ya tashi ranar alhamis da ta shige daga Galveston a Jihar Texas domin shawagin kwanaki 4 cikin teku. A ranar lahadi, wuta ta tashi a dakin da injunan jirgin suke, ta lalata babbar hanyar lantarkin wannan jirgi, abinda kuma ya haddasa hanyoyin samun ruwa. Wannan abu ya faru kilomita 240 cikin teku daga gabar yankin Yucatan na kasar Mexico.

Wasu fasinjojin sun ce a kan fafarandar jirgin suke kwana saboda wari da kuma zafi a cikin dakunan jirgin saboda rashin wuta.
XS
SM
MD
LG