Accessibility links

Wata Kungiya Ta Dauki Alhakin Sace 'Yan Kasashen Waje A Jihar Bauci


Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Bauchi, Mohammed Ladan, yana bayani ga 'yan jarida game da tashin bam a harabar majami'ar Harvest Field Church dake Unguwar Yelwa a Bauchi, lahadi 3 Yuni 2012

Wata kungiya mai suna Jama'atul Ansarul Muslimina Fi Biladil Sudan ta bada sanarwar cewa ita tayi awon gaba da 'yan kasashen waje guda bakwai dake aiki a kamfanin gina titi a Najeria.

WASHINGTON, D.C -- Wata sanarwa dake dauke da sharuda guda biyu da kuma sunan Abu Usamatul Ansari, tayi bayanin cewa bisa irin cin mutunci da kasashen turawa suke aikatawa addinin Musulunci a Afghanistan da Mali, kunigyar tana rike da mutane guda bakwai da suka hada da ma'aikata daga kasashen turawa da Lebanon masu aiki da kamfanin Setraco a Najeria.

Wakilin Muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad ya bada bayanin cewa kungiyar ta yi gargadin cewa duk wani yunkuri ko kuma wani shiri daga kasashen turawa ko gwamnatin Najeria da ya sabawa ka'idojinsu zai haifar da abubuwan da suka faru a baya.

Kungiyar bata bayanna ko wadanne abubuwa ne suka faru a baya ba.

A halin da ake ciki, manyan ma'aikatan kamfanin Setraco sun bar garin Jama'are kamar yadda shugaban karamar hukumar, Adamu Aliyu ya shaida wa Muryar Amurka.

"Su turawan da suke rage, wadanda basu fi su uku ba, sune suka tafi Abuja. Amma sauran kananan ma'aikata suna nan." A cewar shugaban karamar hukumar.

Kamfanin Setraco dai na aikin titin Kano zuwa Maiduguri ne a jihar bauci, kuma yana da sansani a garin Jama'are inda ma'aikatan ke kwana.

Jiya Lahadi mun baku rahoton da yace, wasu 'yan bindiga sun kashe maigadin sansanin kamfanin, kuma sun yi awon gaba da mutane guda bakwai.

Satar mutane domin yin garkuwa da su ya zama ruwan dare a Najeria, al-amari wanda aka fi sani da faruwa a kudancin kasar, yanzu ya yadu zuwa kusan ko ina a Najeria.

Najeria kasa mai fama da rashin ayyukanyi, rashin kayan more rayuwa, da lalacewar tsarin tsaro na fuskantar kalubalen tattalin arziki saboda karancin tituna masu kyau, karuwar adadin mutane, rashin kwararru masu horas da ma'akaita wadanda yawacinsu daga kasashen waje suke zuwa, da kuma tasowar kungiyoyi masu tsatsaurrar ra'ayi dake amfani da addini da makamai domin yada manufofinsu.

A watan da wuce ne, wasu 'yan bindiga a Aljeriya su 30 suka yi garkuwa da ma'aikatan kasashen waje masu yawa a wani kamfanin sarrafa iskar gas, kuma hakan ya jawo hankalin duniya baki daya game da haduran da ma'aikatan kasashen waje ke fuskanta. Wannan arangama dai ta kare ne da mutuwar ma'aikatan kasashen waje guda 37, da duka 'yan bindigan su 30 bayan luguden wuta da sojojin kasar Aljerian suka yi musu.

Kwararru sun bayyana cewa rashin kayan more rayuwa kamar tituna na durkusar da tattalin arziki, saboda wahala, da lokacin da ake sharewa wajen sufurin mutane da kaya.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG