Accessibility links

Mun Kama Gwamnan Lardin Raqqa - inji Masu Tawayen Siriya


Wani mutum mutumin mahaifin shugaba Assad kennan a lokacin da ake tunbuke shi.

‘Yan gwaggwarmayar kasar Siriya sun ce sun kama gwamnan lardin Raqqa dake arewacin kasar, bayan sun fatataki dakarun gwamnati daga babban birnin lardin.

Kungiyar kare hakin al’ummar kasar Siriya dake da cibiya a Birtaniya ta bayyana yau Talata cewa mayaka sun kama Hassan Jalili da suka bayyana a matsayin jami’in gwamnati mafi girma da aka kama tunda aka fara tarzomar kin jinin shugaba Bashar al-Assad.

‘Yan tawayen sun kwace wani bangaren birnin Raqqa jiya Litinin, sai dai ‘yan gwaggwarmaya sun ce ana ci gaba da gumurzu a wadansu sassan babban birnin lardin. Birnin dake gabar tekun Eupharates, yana tazarar kilomita 80 kudu da kasar Turkiya.

Yanzu haka ‘yan tawaye sun kwace ikon manyan biranen kasar Siriya da dama da suka hada da Aleppo a arewacin kasar, da wadansu unguwannin Damascus babban birnin kasar da kuma birnin Homs. Wannan wani koma baya ne ga gwamnatin Mr. Assad wadda ta shafe shekaru biyu tana fama da tarzomar da ta rikide ta zama yakin basasa.
XS
SM
MD
LG