Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Syriyawa Miliyan Daya Ne Suka Gudu - inji Majalisar Dinkin Duniya


Yara a makarantan 'yan gudun hijiran Syria, dake Turkiyya.

Majalisar dinkin duniya tace adadin Syriawa da suka gudu suka bar gidajensu saboda rigima da aka share shekaru biyu anayi ya kai Miliyan Daya, a lokacin da wasu miliyoyin suna cikin kasar amma ba a gidajensu ba.

WASHINGTON, D.C - Ofishin ‘yan gudun hiijira na Majalisar Dinkin Duniya ne ya bada wannan rahoto yau laraba, sannan shugaban ofishin Antonio Guterres yace tashin hankaliin Syria ta cigaba da tabarbarewa kuma abun ya kusa zama na inna na ha.

Mafi yawancin ‘yan gudun hijiran suna kasashen Lebanon, Jordan, Turkiyya, Iraqi da masar, kuma gwamnatin wadannan kasashe na shan wahala wajen biyan bukatunsu.

Wata mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya, Sybella Wilkes ta gayawa Muryar Amurka cewa da yawa daga cikin ‘yan gudun hijiran basu da komai, kuma adadin mutanen da guduwa ya zarta yadda ake tsammani.
XS
SM
MD
LG