Accessibility links

Koriya Ta Arewa Na Shirin Yaki


Wata motar bus a birnin Pyongyang rufe da kakin sojoji. Kyodo, Maris 6, 2013.

Alamu na nuna cewa Koriya ta Arewa na shirya mutanenta domin yin yaki da kasar Koriya ta Kudu wadda Amurka ke goyawa baya. Tana haka ne ta boye harkokin sufurin mutane, da kuma watsa labarai masu dauke da sakonnin ‘yan kasa masu goyon bayan aje yaki.

WASHINGTON, D.C - A yau dinnan ne kafofin yada labaran Koriya ta Kudu da Japan suka bada rahotanni da suka ce jami’ai a Pyongyang – babban birnin Koriya ta Arewa sun fara rufe motocin bus da kaki irin na sojoji, wani fasali na taka-tsan-tsan da aka share shekaru masu yawa ba’a gani ba a wannan birni.

A shekara ta 1993 ne lokaci na karshe da aka ga Koriya ta Arewa ta rufe motocin bus da kakin sojoji, bayan da ta cire kanta daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi.

Gidan talabijin na gwamtin Koriya ta Arewan ya nuna hotunan bidiyo na mazauna birnin Pyongyang masu fadar albarkacin bakinsu, dangane da barazanar da Koriya ta Arewan tayi na yin watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta na wucin gadi da Amurka wanda aka rattaba wa hannu a shekarar 1953 bayan ran 11 ga wannan wata na Maris.

Ma’aikatar tsaron koriya ta kudu tayi alwashin daukatar mataki mai karfi idan har koriya ta arewa ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta na wucin gadi dake tsakaninsu na tsawon shekaru 60.

Janar Kim Yong-hyun yau laraba yace Koriya ta Kudu a shirye take ta kai hari ga inda wannan barazana ta samo asali, da kuma inda ake bada umarni na wannan barazana idan dai har Koriya ta arewan tayi amfani da karfin soji.
XS
SM
MD
LG