Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nelson Mandela Yana Samun Sauki


Nelson Mandela

Ofishin shugaba Jacob Zuma ya ce Mr. Mandela yana cikin raha sosai, kuma a yau Jumma’a da safe ma, yayi karin kumallo da abinci sosai.

An bayar da rahoton cewa tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Nelson Mandela, yana samun sauki, kwanaki biyu a bayan da aka kwantar da shi a asibiti a saboda wani ciwon da ya kama huhunsa.

Ofishin shugaba Jacob Zuma ya ce Mr. Mandela mai shekaru 94 da haihuwa, yana cikin raha sosai, kuma a yau jumma’a da safe ma, yayi karin kumallo da abinci sosai.

Shugaba Zuma ya fada jiya alhamis cewa Mr. Mandela yana murmurewa, yana mai cewa bai kamata hankalin ‘yan Afirka ta Kudu ya tashi ba.

Amma hankulan mutane da dama yana tashe a kasar ta Afirka ta Kudu, inda ake daukar Mandela a zaman gwarzo na kasa.

A ranar laraba aka garzaya da Mr. Mandela zuwa wani asibitin da ba a bayyana ba. A watan Disamba ma, an kwantar da Mandela a asibiti na tsawon makonni uku a saboda wani ciwon da ya kama huhunsa, da kuma dutse a matsarmamarsa.

Jiya alhamis shugaba Barack Obama na Amurka yace ya damu sosai da lafiyar Mr. Mandela, mutumin da ya bayyana a zaman gwarzo, kuma abin koyi.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG