Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tankiya Na Kara Tsanani A Tsakanin Kasashen Koriya


Shugaba Park Geun-Hye ta Koriya ta Kudu

Shugabar Koriya ta Kudu ta umurci dakarun kasar da su mayar da martani nan take, kuma mai tsanani kan duk wata t6sokana daga Koriya ta Arewa

Sabuwar shugabar Koriya ta Kudu ta ce tana bayar da muhimmancin gaske ga barazanar dake kwararowa daga makwabiyarta Koriya ta Arewa, barazanar da mutane da dama ke nuna fargabar cewa zata iya haddasa fada a yankin.

A ganawar da ta yi da manyan jami’an tsaron kasa yau litinin, shugaba Park Geun-hye, ta umurce su da su mayarda martani mai tsanani, kuma nan take ga duk wata tsokanar fada daga Koriya ta Arewa ba tare da yin la’akari da tasirin da hakan zai yi a fagen siyasa ba.

Wannan gargadi na shugaba Park yana zuwa a yayin da majalisar dokokin jeki-na-yi-ki ta Koriya ta Arewa ta gudanar da taronta na shekara, kuma kwana guda a bayan da shugabannin jam’iyya mai mulkin kasar suka lashi takobin fadada makamansu na nukiliya.

Hukumomi a Pyongyang sun kara zaman tankiya a saboda barazanar da suka sha jaddadawa kan Koriya ta Kudu da Amurka domin fusatar da suka yi game da atusayen soja na hadin guiwa da kasashen biyu ke yi, da kuma takunkumin da Kwamitin Sulhun MDD ya kara kakabawa kasar bayan da ta yi gwajin nukiliya na uku.

Jiya lahadi, wasu jiragen saman yaki guda biyu na Amurka samfurin F-22 Raptor sun tashi daga sansanin mayakan sama na Kadena dake tsibirin Okinawa a Japan, zuwa sansanin mayakan sama na Osan, mai tazarar kilomita 65 a kudu da Seoul. Wadannan jiragen saman kai farmaki wadanda aka shafe da wani sinadarin dake hana na’urorin sunsuno jirage hango su, zasu shiga cikin atusayen sojan da ake ci gaba da yi har zuwa karshen watan nan.
XS
SM
MD
LG