Accessibility links

Janar Abdurrahman Bello Dambazau yace ba aikin soja ne zama a kan titi yana binciken mutane da ababen hawa ba.

Tsohon babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Janar Abdurrahman Dambazau mai ritaya, yace ba aikin soja ne ya zauna a titi yana binciken mutane da ababen hawa ba, aikin dan sanda ne. Yace ko su 'yan sandan ma, bai kamata a ce sun zauna dindindin su na wannan aikin ba.

Janar Dambazau, wanda ke halartar wani taron da Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka ta shirya a Washington, DC, kan batun Tsaro a Yankin Sahel na Afirka ta Yamma, ya fadawa Muryar Amurka cewa idan har lamari ya baci ana bukatar kai soja wani wuri, to tilas ne a tabbatar da cewa an kai shi na wani dan karamin lokaci kawai, sannan a maida shi barikinsa.

Tsohon hafsan sojan na Najeriya, yace tilas ne sojan da aka kai wani wuri domin aikin tsaro, ya mutunta ya kuma karrama mutanen wurin da addinininsu da al'adunsu. Ya ce bakin ci9kin da jama'a ke yi na ganin yadda sojoji ke musguna musu, shi yasa suke kiraye-kirayen da a janye su daga wurare irinsu Maiduguri da Kano wasunsu.


Ya ce barin sojojin a yanzu ya zamo dole, tun da babu wadanda za a iya maye gurbinsu da su. Sai dai yace ya kamata a samar da horo da kayan aikin da ya dace ga 'yan sanda domin su dauki nauyin gudanar da irin wannan aikin da tun farkio nasu ne ba na soja ba.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG