Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Sojojin Chadi Uku A Mali


Sojojin uku sun mutu yau jumma'a a lokacin da dan kunar bakin wake ya tayar da bam a wata kasuwa a arewacin Mali

An kashe sojojin kasar Chadi uku yau Jumma'a, a lokacin da wani dan harin kunar bakin wake ya tayar da bam a cikin wata kasuwa a yankin arewacin Mali.

Shaidu da kuma 'yan sanda sun ce wannan dan kunar bakin wake ya auna sojojin ne a birnin Kidal dake arewacin Mali, ya kashe su da kuma kansa.

Wasu sojojin su hudu sun ji rauni tare da fararen hula da dama a wannan harin.

Wannan harin kunar bakin wake shi ne na uku irinsa a birnin Kidal, tun watan Janairu, lokacin da Faransa ta jagoranci wani farmakin da ya 'yantar da wannan birni tare da wasu da dama a arewacin kasar daga hannun tsagera 'yan kishin Islama.

Akwai sojojin Faransa su dubu 4 dake gwabzawa da tsageran. Sannan akwai sojojin Mali da na kasashen Afirka, ciki har da dubu 2 daga Chadi dake yakar tsageran.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG