Accessibility links

Tsagera Sun Kai Hari Kan Kolejin Gwamnati Ta Buni Yadi - Sun Kashe Dalibai Da Dama


Wani dan sanda yana duba gine gine da ababan hawa da kuma makamai bayan harin da kungiyar Boko Haram ta kai a Damaturu ranar 25 da 25 ga watan Oktoba. An dauki hotunan ranar 28 ga watan Oktoba, 2013.

Har yanzu ba a san adadin wadanda suka mutu ba a lokacin da 'yan bindigar da ake jin 'yan Boko Haram ne suka kai farmaki kan kolejhin gwamnati ta Buni Yadi

Rahotannin dake fitowa daga yankin arewa maso gabashin Najeriya sun ce 'yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kai farmaki kan kolejin gwamnati dake Buni Yadi a yankin karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

Hukumomi sun tabbatar da abkuwar hakan, sun kuma ce yanzun nan ake ciro gawarwakin wadanda suka mutu, don haka babu adadi na wadanda suka rasa rayukansu ya zuwa yanzun.

Wasu daliban da dama sun samu tserewa.
XS
SM
MD
LG