Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakatare Kerry Zai Shiga Tsakani a Sudan ta Kudu


​Sakataren harakokin wajen Amurka, John Kerry, na kokarin shirya tattaunawar kai tsaye tsakanin shugaban kasar Sudan ta Kudu da madugun 'yan tawaye, da fatan kawo karshen tashin hankalin da ke k'ara ta'azzara a kasar.

A yau Jumma'a Kerry ya isa Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu kuma har ya gana da shugaba Salva Kiir. Bayan ganawar ya ce Mr.Kiir na shirye ya halarci tattaunawar zaman lafiyar da za a yi a kasar Ethiopia a makon gobe, wadda ake kyautata fatan za ta hada har da madugun 'yan tawaye da kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar.

Ya ce ya shirya tattaunawa da Machar ta wayar talho a wani lokaci can a yau Jumma'a.

Sakataren harakokin wajen na Amurka yayi kira ga dukan su biyu cewa su ki goyon bayan hare-haren da ake kaiwa fararen hula saboda dalilan kabilanci. Haka kuma Kerry na kokarin kulla yarjejeniyar da za ta bayar da dama, nan kusa a tura sojojin kungiyar kasashen Afirka masu tsaron zaman lafiya, su je su taimaka wajen dakile fad'an kuma su kare lafiyar fararen hula.

Kerry na rangadi a kasashen Afirka da dama da nufin mayar da hankali kan matsalolin tsaro da hakkokin bil Adama.

Idan Kerry ya koma Addis Ababa zai gana da shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud domin su tattauna hanyoyin yakar kungiyar al-Shabab mai alaka da al-Qaida.

Gobe Asabar zai kasar Jamahuriyar Demokradiyar Kwango inda zai gana da shugaba Joseph Kabila. Ranar litinin Mr.Kerry zai dawo nan birnin Washington, DC, bayan ya yada zango a kasar Angola.
XS
SM
MD
LG