Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kowa Yana Amfani da Kowa a Najeriya


Goodluck Jonathan yana jawavi ga wakilai

Idan ba’a samu wani sauyi ba, za’a gama taron kasa da ake gudanarwa a Abuja, inda batun arzikin kasa yafi daukan hakali, kuma hakan baya rasa nasaba da yanda kowane bangare ke neman kare muradun sa.

Janar Dan Ali, wakili ne a taron kasa da ake yi yace “ akwai wadanda suka zo da ajandar raba kasar nan amma cikin yardan ubangiji da aka taru aka cewa bah aka ya kamata ba.”

Yakar da cewa an gano cewa kowa yana amfani da kowa a kasar nan ba wanda bai son wani a ciki, dama idan yau suka fito da wannan gobe zaka ji wani kuma ya fito to har Allah yasa muka samu aka rurrufa kwamitoci suka rufe aka fito da mahawara kowa ya yarda da juna.

Zargin da akeyi cewa an bada toshiyar baki don goyon bayan son zuciya ya jawo kace nace da nesata kan daga batun. Ya dai zama wajibi a mika duk abunda taron ya zarta ga majalisa don mahawara na amicewa ko akasin haka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG