WASHINGTON, DC —
Majalisar dokokin Jihar Adamawa ta zartas da tsige gwamna Murtala Nyako, dan jam'iyyar APC, daga kan kujerarsa ta gwamna.
Jim kadan kafin majalisar ta dauki wannan matakin, mataimakin gwamnan Jihar, Bala James Ngilari, yayi murabus daga kan kujerarsa, abinda ya sa majalisar ba ta ma karanta takardar tsige shi ba.
A yanzu haka, ana kokarin rantsar da kakakin majalisar dokokin jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, dan jam'iyyar PDP daga mazabar Madagali, a zaman mai rikon mukamin gwamnan jihar.