Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan PDP Na Majalisar Nassarawa Ma Zasu Tsige Al-Makura

Gwamna Tanko Al-Makura na Jihar Nassarawa
Gwamna Tanko Al-Makura na Jihar Nassarawa

A Jihar Nassarawa , ‘yan majalisar dokoki 'yan jam'iyyar PDP sun ce zasu wallafa takardar tuhumar gwamna Tanko al-Makura na jam’iyyar APC a jaridu, a sabon yunkurin da suka kama na tsige shi.

An ce sau biyu akawun majalisar dokokin yana yunkurin mikawa gwamna takardar tuhumarsa da 'yan majalisar keyi, amma bai samu shiga ba. Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Mohammed Baba Ebako, yace bayan wallafa takardar a jaridu da mako guda, zasu ci gaba da yunkurin tsige gwamnan idan bai ba su amsar da ta gamsar da su ba.

Sai dai kuma kwamishinan yada labarai, Mohammed Hamza Elayo, yace ba su ga ka’idojin kasafin kudin da ‘yan majalisar suka ce sun kafa suke kuma zargin gwamnan da karyawa ba.

Haka kuma wasu matasa sun shirya zanga-zanga a jihar domin nuna rashin yardarsu da wannan mataki na majalisar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG