Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Saman Fasinja Na Malaysia Ya Fado Da Mutane 295 Cikinsa

Ma'aikacin kashe gobara na Ukraine yana kokarin kashe wutar dake ci a inda jirgin Malaysia ya fado kasa yau alhamis, 17 Yuli 2014. Gawarwakin fasinjoji ne warwatse a wurin.
Ma'aikacin kashe gobara na Ukraine yana kokarin kashe wutar dake ci a inda jirgin Malaysia ya fado kasa yau alhamis, 17 Yuli 2014. Gawarwakin fasinjoji ne warwatse a wurin.

Kafofin labarai na Rasha sun ce wani jirgin saman fasinja na Malaysia da ya taso daga Amsterdam kan hanyarsa ta zuwa Kuala Lumpur ya fadi a gabashin Ukraine, inda ake gwabza fada a tsakanin sojojin gwamnati da na 'yan aware.

Wani jami'in ma'aikatar harkokin cikin gidan Ukraine, Anton Gerashchenko, yace an harbo jirgin saman fasinjar ne da wani makami mai linzami na harbo jiragen sama.

Kamfanin safarar jiragen saman Malaysia ya fada ta shafinsa na Twitter cewa a yau alhamis, sadarwa ta tysinke a tsakaninsa da wannan jirgi a samaniyar kasar Ukraine. Jirgin, kirar Boeing-777, yana dauke da fasinja 280 da kuma ma'aikata 15.

Fadar shugaban Amurka ta White House ta ce jami'an Amurka su na tuntubar na Ukraine game da rahoton wannan lamarin, amma ba ta yi karin bayani ba.

Madugun 'yan awaren Ukraine, Alexander Borodai, ya zargi rundunar sojojin sama ta Ukraine da laifin harbo wannan jirgin fasinja na Malaysia. Ya fada ta Twitter cewa 'yan tawayen ba su da makamin da zai iya harbo jirgin saman dake tafiya kimanin kilomita 10 a sama da doron kasa. Gwamnatin Ukraine ta musanta cewa da hannun sojojinta.

Firayim minista Najib Razak na Malaysia, yace zai kaddamar da bincike nan take kan faduwar jirgin. Ministan tsaron Malaysia, Hishamuddin Hussein, yace babu tabbacin cewa an harbo jirgin ne.

Wannan shi ne mummunan bala'i na biyu dake fuskantar kamfanin jiragen saman Malaysia a wannan shekara. Wani jirgin kasar mai lambar tafiya MH-370 ya bace har yau babu wanda ya san inda yake, dauke da mutane 239 a kan hanyarsa ta zuwa Beijing daga Kuala Lumpur.

XS
SM
MD
LG