Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekau, Mune Ajalinka Insha Allah In Ji 'Yan Kato-Da-Gora


Wasu matasa 'yan banga suka tsaya don a dauki hotonsu a Maiduguri, 11 Yuni, 2013.
Wasu matasa 'yan banga suka tsaya don a dauki hotonsu a Maiduguri, 11 Yuni, 2013.

Matasa 'yan bangar dake yakar Boko Haram a Jihar Borno, wadanda aka fi sani da sunan 'Yan Kato-Da-Gora ko Civilian JTF, sun lashi takobin ci gaba da farautar 'yan ta'addar da suka fitini al'ummar arewa maso gabashin Najeriya.

A hirar da suka yi da 'yan jarida a Maiduguri domin karyata rahotannin cewa 'yan Boko Haram sun kwace garin Bama, matasan sun lashi takobin murkushe 'yan Boko Haram har ma wani cikinsu ya sha alwashin cewa sai sun ga bayan Abubakar Shekau, mutumin dake ikirarin cewa shi ne shugaban kungiyar ta Boko Haram.

Haka shi ma mai ba su shawara a kan harkokin shari'a, barrister Jibrin Gunda, yace lallai hankulan jama'a sun tashi a garin Bama, amma kuma har yanzu sojojin Najeriya ne suke rike da barikin soja na garin da kuma cikin gari.

Yace babu gaskiya a cikin rahotannin da wasu ke yadawa cewa 'yan Boko Haram sun kame garin na Bama.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG