Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Binne Sa’adatu Fawu a Abuja


Hoton Sa'adatu Muhammaed Fawu

Allah Yayi wa Sa’adatu Muhammad Fawu rasuwa a yammacin jiya Talata, a wani asibiti dake birnin Tarayyar Najeriya Abuja.

Anyi wa wakiliyar ta Muryar Amurka a arewa maso gabashin Najeriya sutura a Makabartar Gudu, dake kusa da unguwar ‘yan majalisa a Abuja.

“Lokaci ne Yayi mana, na muzo duniya, da kuma lokaci da zamu bar duniya. Allah Shi Ya san dalilin barin duniyar nan”, a cewar Imam Shehu na babban Masallacin Abuja kennan a lokacin da yake addu’a gaban kabarin Sa’adatu Muhammad Fawu.

Sa’adatu dai ta fara aiki ne da Muryar Amurka a shekara ta 2006, daga ofishin labarun lafiya a Kano.

Alhassan Fawu, dan uwan marigayiyar ne a Abuja wanda yayi magana da Muryar Amurka yana kuka.

“Allah Ya sa ta cika da Imani, mutanen VOA, Allah Ya baku hakuri, domin wannan rashinmu ne dukanmu.”

Kafin Sa’adatu ta fara aiki da Muryar Amurka, tayi aiki ne a Sashen Talabijin na Hukumar Labaru ta Jihar Gombe, wato Gombe Media Corporation.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:09 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG