Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Yi Nasara Kan Kotun Kasa Da Kasa-Inji OMar al-Bashir Na Sudan


Omar al-Bashir, shugaban kasar Sudan.

Mai gabatar da kara a kotun tace zata karkata akalar binciken zuwa wasu sassa.

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir yana ikirarin galaba kan kotun kasa da kasa mai hukunuta laifuffukan yaki, bayan da mai gabatar da kara a kotun ya bada sanarwar dakatar da bincike kan laifuffukan yaki da aka aikata a yankin Darfur.

Da yake magana a yau Asabar a khartoum, shugaba Bashir yace al'umar kasar sun sami "galaba"kan kotun kasa da kasar da hkumomin kasar suka ki mika jami'an kasar da ake tuhuma da aikata laifuffukan yaki a yankin Darfur ga kotun da ya kira ta "ta mulkin mallaka".

Yace kotun ta amince cewa ta "gaza" a yunkurin ta na auna bincikenta akansa.

A jiya jumma'a ce dai babbar mai gabatar da kara a gaban kotun Fatou Bensouda tace bata da sauran zabi "illa ta jingine bincike kan shugaba al-Bashir" ta karkata kudaden wajen wasu ayyuka na daban.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG