Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barazanar Yajin Aiki A Flato-Ba Albashi Tun Watan 10-NLC


'Yan jarida suka gewaye shugaban kungiyar kwadago na Najeriya Abdulwahid Umar a Abuja.
'Yan jarida suka gewaye shugaban kungiyar kwadago na Najeriya Abdulwahid Umar a Abuja.

Kungiyar kwadago reshen jihar Flato, ta baiwa gwamnati wa'adin mako biyu ta biya musu bukatunsu ko kuma.......

Kungiyar kwadagao ta kasa a Najeriya,watau NLC a takaice, reshen Flato, tayi barazanar zata shiga yajin aiki, muddin har wa'adin mako biyu data baiwa gwamnati suka cika, gwamnati bata biya musu bukatunsu ba.

Shugaban kungiyar Jibrin Bancir, wanda ya bayyana haka a tattaunawa da manema labarai a Jos fadar jihar, ciki harda da wakliyar Sashen Hausa Zainab Babaji, yace rabon gwamnati da biyan albashi ga ma'aikatan jihar tun a watan oktoban bara. Su kuma wadanda suke karbar kudin fansho, rabon da a biyasu tun watan bakwai na bara.

Bugu da kari Mr. Bancir yace, akwai ma'aikatan kananan hukumomi wadanda suka bar aiki tun shekara ta 2011, amma har zuwa yanzu ba'a biya su hakkokinsu ba.

Da yake magana, wani jigo a kungiyar ma'aikatan dakon man fetur reshen jihar, komorade Ado Ali, yace a shirye kungiyarsa take ta shiga wannan yajin aiki,domin a-sani-cewa, suma suna karkashin kungiyar kwadago.

A nata bangaren, shugaban ma'aikata na gwamnatin jihar, Ezekeiel Daliop, yace gwamnati tana bakin kokarinta na ganin an biya ma'aikatan.

Tuni dai ma'aikatan kiwon lafiya dake karkashin gwamnatin jihar, da kuma na tarayya suke cikin yajin aiki. Haka ma wadanda suke bangaren shari'a.

SAUTI: Barazanar yajin aiki a Flato, ba albashi tun watan 10-NLC-3' 34" http://bit.ly/1ukeY0J

HOTO: Abdulwahid Umar, shugaban kungiyar kwadago.

#Hausa #Nigeria

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG