Accessibility links

Shugaba Buhari Ya Fara Nada Jami'an Gwamnatinsa

  • Aliyu Imam

Sabon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

Tuni Shugaban ya bada sanarwar nada mai bashi shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina da babban jami'in yada yada labarai Mallam Garba Shehu.

Banda Femi Adeshina, wanda kamin nadin da shugaba Buhari ya masa, shine babban Editan jaridar "The Sun".Shugaban ya kuma baiwa Mallam Shehu Garba babban jami'in yada labarai, wanda kamin wannan nadin, shine babban jami'in yada labarai a kwamitin yakin neman zaben shugaba Buhari. Kamin nan, yayi aiki da mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Sauran wadanda Shugaba Buhari ya nada sun hada da Ambasada Lawal Abdullahi Kazaure, a matsayin babban mai kula da baki, ko Chief of Protocol, da turanci. Ya kuma nada babban dogarinsa ko ADC, wanda saboda yanayin aikinsa ba'a bayyana sunansa ba.

Da yake karin haske kan wadannan nade nade, Mallam Shehu Garba, ya yaba da nade naden, ya kuma bayyana fatar ba zasu baiwa marada kunya ba.

Gameda lokacinda shugaban zai bayyana karin nade nade kamar majalisar ministocinsa, Mallam Garba Shehu yace a saurara kadan.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG