Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Kori Manyan Hafsoshin Sojan Kasar


Wadanda aka kora sun hada da hafsan sojojin tsaro, Air marshall Alex Badeh, da kuma manyan hafsoshin sojan ruwa da na sama da na kasa

Shugaban Najeriya, Janar Muhammadu Buhari, ya kori manyan hafsoshin sojan kasar, kuma ana shirin bayyana sunayen wadanda zasu gaje su.

Wakilin Muryar Amurka, Umar Faruk Musa, yace kakakin shugaban, Femi Adesina, ya fada cikin tattaunawarsa da 'yan jaridar fadar shugaban fazu cewa lallai an sallami manyan hafsoshin kuma ana shirin fitar da sanarwa kan wadanda zasu maye gurabunsu.

Da ma an jima ana tsammanin cewa sabon shugaban na Najeriya zai saukar da manyan hafsoshin, musamman ma ganin yadda har yanzu an kasa shawo kan rigimar Boko Haram duk da makudan kudaden da aka akashe kan harkar tsaro a kasar.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG