Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rusa Rundunar Tsaro Ta Fadar Shugaban Kasa A Burkina Faso.


Shugaban wucin gadi a Burkina Faso, Michel Kafando.

Shugaba Michael Kafando ne ya saka hanu kan dokar data rusa rundunar jiya jumma'a.

A Brukina Faso shugabannin kasar sun rusa rundunar tsaro ta fadar shugaban kasa,wacce ta ayyana juyin mulki makon jiya wanda bai sami nasara ba.
Shugaban wucin gadi na kasar Michel Kafando ne ya sanya hanu kan dokar da ta wargaza runduar a maraicen jiya jumma'a, al'amari da aka nuna ta talabijin. Hakan nan shugaba Kafando ya kori ministan tsaro kanal Sidi Pare.

Ranar Laraba aka sake maida gwamnatin wucin gadin kasar karkashin shugabancin Micel kafando da PM Yacouba Isaac Zida.

Madugun sojojin da suka ayyana juyin mulkin Janar Gilbert Diendere yayi murabus bisa umarnin da kungiyar ECOWAS, tareda matsin lamba daga rundunar sojojin kasar da kuma jama'ar Burkina Faso.

Tuni dai Janar Diendere yayi nadamar ayyana jiyun mulkin, wanda suka yi domin nuna fushinsu kan hana magoya bayan tsohon shugaban kasar Blaise Comaore yin takara.

Kamin juyin mulkin kasar tana shirin gudanar da zabe ranar 11 ga watan Oktoba mai zuwa, shekara daya bayan da aka hambare gwamnatin Blaise Compaore. Babu tabbas ko ha r yanzu za'a gudanar da zaben kamar yadda aka ayyana tun farko.

Shugabannin kungiyar ECOWAS sun bada shawarar a gudanar da zaben ranar a 22 ga watan Nuwamba,kuma a kyale magoyan bayan tsohon shugaban kasar suyi takara.

Kungiyoyin farar hula da jam'iyun siyasar kasar sun bayyana rashin goyon bayansu kan shirin yin afuwa ga wadnada suka shirya juyin mulkin.

PM kasar Zida yace har yanzu ba'a yanke shawara kan makomar madugun juyin mulki Janar Diendere ba, yace za'a tantance mataki da gwamnati zata dauka akansa da zarar an kammala gudanar da bincike.

XS
SM
MD
LG