Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace Shanu 150 a Jahar Taraba


Shanun Fulani.

Rahotanni daga Jahar Taraban Najeriya na cewa an sace akalla shanun wasu Fulani guda 150 inda ake zargin al’umar Jukunawa da yin awon gaba da shanun.

“Jiya da misalin karfe biyu na rana, Jukunawa sun zo sun sami shanu na a jeji, sun zo sun tattaru gaba daya babu yaran babu shanun, shanun nan za su kai 150.” In ji Bafulatanin da ya mallaki shanun, wanda kuma bai bayyana sunansa ba.

Matsalar satan shanu, batu ne da ya kusan zama ruwan dare a Najeriya inda aka samun aukuwar lamarin a juhohi irinsu Pilato da Nasarawa da Benue da ma wasu juhohi da ke arewa maso yammacin kasar.

“Muna mamakin wannan abu, mun yi kuka ga gwamnatin Jaha, ba sau daya ba ba sau biyu ba, shi gwamna mun yi zama da shi a Wukari ya ce a yi hakuri zai kare dukiyar mu zai kare rayukanmu, to amma gashi har yau ana kashe mu a dauke mana dukiya, ban ga kamar gwamnatin ta na da niyyar kare mu ba.” In ji shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah na Jahar Taraba, Alhaji Ummaru Mafindi.

To sai dai kungiyar hadin kan Jukunawa a jahar ta Taraba, ta musanta cewa da saninta ne ake wannan sace-sacen.

“Zai zama babban kuskure a yi irin wannan zargi, gaba daya a ce Jukunawa, har yanzu kungiyar hadin kan Jukunawa na kan bakar ta na cewa a yi zaman lafiya tsakanin kabilu da ke zaune, babu ruwanmu da wanda zai tada mana da hankali, ko kuwa ya je ya yi sata da sunan Jukunawa.” In ji shugaban kungiyar hadin kan Jukunawa ta Najeriya, Mr. Bako Benjamin.

Ga Ibrahim Abdulaziz da karashen rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG