Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Lagos Ta Hana Gangami Lokacin Kirsimeti


Wasu Mata a Lagos cikn shiga irin ta al'adar su suke murnan cika shekaru 55 da samun yancin Najeriya

Gwamnatin jihar Ikko ta bada dokar hana gangami da duk wadansu taruka da ka iya barazana ga tsaron lafiyar al’ummar jihar.

A cikin sanarwar da gwamnatin jihar ta bayar wadda kwamishin watsa labarai na jihar ya jadada, gwamnatin tace ta dauki wannan matakin ne domin kare lafiyar al’umma musamman a wannan watan na Disamba da ake shagulgulan kirsimeti.

Sai dai wannan doka da gwamnatin ta fitar ya yi karo da ra’ayoyi na al’umma. Musamman masu fafatukar kare hakin bil’adama. Wata mai Magana da yawun irin masu wannan ra’ayin tace, ko shakka babu akwai karuruwar ayyukan ta’addanci a kasar, dai dai yace, ya kamata hukumomi su sani cewa,a kokarin da suke yi na dakile wannan matsala, bai kamata su tauye hakin al’umma na walwala ba.

Wani mazaunin Lagos da Sashen Hausa ya yi hira da shi yace ko kadan ba za a amince da wannan takunkumin da hukumomi ke amfani da shi wajen takura al’umma ba. Yace ko kadan wannan bai dace ba domin akwai ‘yanci na gudanar da taro, akwai ‘yanci na fadin albarkacin baki.

Yayinda wadansu ke kushewa wannan dokar, wadansu suna gani ta dace domin akan sami rahotannin sace sace da fashi a wadannan lokuta.

Ga rahoton da Wakilin Sashen Hausa Babangida Jibril ya aiko daga Ikko.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

XS
SM
MD
LG