Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Friministan Uganda Ya Yiwa 'Yan Kasar Aikawarin Gudanar Da Zabe Lafiya


Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni.

Wannan kalamin nashi yana zuwa ne yayinda wasu ke fara bayyana fargabar cewa kila tashin hankali ya barke a lokacin zaben

Firayim ministan, Ministan Uganda, Ruhakana Rugunda, ya tabattarwa ‘yan kasar cewa zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar da za’ayi gobe Alhamis, za’ayi shi lafiya, a gama shi lafiya, don haka yana kira akan dukkan ‘yan kasar da su fito su jefa kuri’unsu bada fashi ba.

Wannan kalamin nashi yana zuwa ne yayinda wasu ke fara bayyana fargabar cewa kila tashin hankali ya barke a lokacin zaben.

Mai yiuwa ne wannan ba zai rasa nasaba da matakin da ‘yansandan Uganda suka dauka jiya Talata ba, akan madugun ‘yan adawa na kasar, Kizza Besigye na jam’iyyar FDC wanda suka toshewa hanya, suka hana shi gudanarda kyamfen dinsa a wasu unguwanni na birnin Kampala.

Firayim minista Rugunda yace abinda ya faru abin a yi nadama ne, amma ya jadadda cewa bai kamata Besigye da mutanensa su nemi yin taron lacca a tsakiyar birnin na Kampala ba.

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG