Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana binciken Sarkozy tsohon shugaban kasar Faransa


Nicolas Sarkozy tsohon shugaban kasar Faransa

Ana bincike tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy bisa hannunsa a wata badakalar kudaden da aka kashe a yunkurin da ya yi na sake tsayawa takarar shugabancin kasar.

A yau Talata Sarkozy ya bayyana a gaban wata kotu, domin amsa tambayoyi kan zargin da ake mai na cewa ya hada kai da wani kamfani mai zaman kansa wajen boye yawan kudaden da ya kashe a lokacin yakin neman zabensa, wadanda aka ce sun wuce ka’ida.

Ana zargin tsohon shugaban kasar da kashe fiye da dala miliyan 25 da aka kayyadewa kowane dan takara a lokacin.

Sarkozy ya kasance shi ne shugaban jam’iyyar kwanzavativ wacce yanzu ake kiranta The Republicans, ya na kuma kokari ne ya daidaita kansa domin yin takara a zaben shekara mai zuwa.

Shi dai Sarkozy ya fadawa kotun cewa sam bashi da masaniyar badakalar boye yawan kudaden da ya kashe a kamfen dinsa.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG