Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kamala Gudanar Da Kayayyakin Zaben Nijar a Kano


zaben Nijar a Najeriya

Hukumar zaben kasar Nijar ta gabatar da kayayyakin aikin zabe a Kano

An kammala gudanar da kayayyakin zaben Nijar a Kanon Najeriya, inda wakilan jamiyyun siyasun suka bayyana gansuwar su ga yadda ake tafiyar da gudanar da zaben nagobe.

Ko da yake karamar jakadiyar Nijar a Kano ta bayyana cewa hukumomin Najeriya sun taimaka musu ainun sai dai ba'a yi musu adalci ba domin kuwa a Najeriya a jihohi bakwai ne kadai aka yi wa ‘yan Niger rigistan katin zabe.

Hukumar zaben Nijar ta gabatar da kayayyakin aikin zabe da za’a gudanar a gobe lahadi daga karfe 7:00 na safe zuwa karfe 7:00 na yamma.

Daga cikin mutane 708, da aka yiwa rajistan zabe mutane 451, ne kawai suka karbi katin zaben su, inda ragowar Katina 284, har ya zuwa yanzu ba’a karbe sub a.

Daga cikin shirye shiryen zaben masu jefa kuri’un su a gobe kafi a barsu su shiga harabar jakadancin Nijar sai sun nuna katunan zaben su da wani katin shedawarsu cewa su ‘yan asalin jamhuriyar Nijar ne , tuni dai aka kawo akwatuna guda biyu da za’a gudanar da zaben dasu.

Ko da yake wasu daga cikin ‘yan jamiyyun sun ce suna da ja da yanda za’a gabatar da takardan haifuwa wajen jefa kuri’a yayin da suka ki amincewa da wannan kudiri.

Karamar jakadiya jamhuriyar Nijar a Kanao Hajiya Rabi Abdu tace babu matsala ga duk wanda yayi rajista sunan sa ya fito bisa kundin zabe idan ya zo da katin da akayi masa rajista zai yi zabe.

XS
SM
MD
LG