Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Papa Roma da Trump sun shiga takunsaka


Donald Trump dan jam'iyyar Republican

Yayinda da 'yan takarar neman jam'iyyarsu ta tsayar dasu shiga zaben shugaban kasar Amurka suke faman fafutikan neman kuri'u sai gashi wata sabuwa ta kunno kai.

Fafutikar neman zaben dai a nan Amurka ya shiga wani yanayi da ba'a taba gani ba inda 'yan takaran suke mayar wa juna kalamu da zazzafan lafazi akan yadda za'a hana bakin haure shigowa kasar da kuma abun da za'a yi da wadanda suke cikin kasar.

Muhawara ta yi zafi tsakanin Donald Trump wanda yake kan gaba cikin 'yan takarar jam'iyyar Republican . A cikin wannan halin ne Papa Roma Francis shugaban darikar Katolika ya soki Donald Trump wanda yace baya tsammanin Kirista ne.

Kalamun na Papa Roma Francis sun mamaye faggen siyasa da kafofin labaru. Kowa ya mayarda hankali akan furucin Papa Roman.

Yayinda yake komawa gida a cikin jirgin sama bayan ya kammala ziyara zuwa Mexico wani dan jarida ya tambayi Papa Roman akan shirin Trump na gina katafariyar katanga tsakanin Amurka da kasar Mexico, sai Papa Roman yace "Duk wanda yake tunanen gina katanga ba mutane ba, ba gina zumunci tsakanin al'umma ba to ba Kirista ba ne"

A nashi kalamun na mayarda martani hamshakin attajirin Donald Trump jiya Alhamis a jihar South Carolina yace abun kunya ne Papa Roma ya kawo shakku akan bangaskiyar wani game da addininsa. A taron 'yan takaran jam'iyyar Republican da suka yi aka kuma baza ta tashar talibijan din CNN da duk duniya ta gani jiya Alhamis Trump ya dan yi sassauci bisa ga matsayin da yake dauka da kafin kalamun Papa Roman. Yace yana girmama Papa Roma Francis . Yace yana ganin an ba Papa Roman wani labari ne daban da manufar shi Trump akan gina katangar.

XS
SM
MD
LG