Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Ta Kudu Ce Kasar Da Shugaban FIFA Ya Fara Ziyarta A Afirka


Infantiano ya gana da shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir

Sabon shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino ya zabi Sudan ta kudu a matsayin kasa ta fari da zai fara zuwa a Afrika biyo bayan zaben sa da aka yi makonni 3 da suka gabata.

Gianni ya fadawa manema labarai a Juba jiya laraba cewa zai yi aiki da hukumar kwallon kafar Sudan ta kudu don daga martabar kwallon kafa a kasar. Haka kuma ya hallarci wasan da Sudan ta kudu ta yi da Janhuriyar Benin inda Benin ta tashi da ci 2 itaka kuma Sudan ta kuda ta sami daya.

Infantiano ya gana da shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir a lokacin da ya isa Juba, Infantiano ya ce su biyun sun tattauna akan yanayin wasn kwallon kafa a kasar da ke kan gwagwarmaya.

XS
SM
MD
LG