Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Na Bincike Kan 'Yan Taiwan Da Kenya Ta Tasa Keyar Su Gida


‘yan kasarTaiwan da yawan su ya kai 45 a mayar dasu kasar China a tsakanin ranakun littini da talata

Kasar China tace tana nan tana binciken tawagar wasu ‘yan Taiwan da kasar Kenya ta tasa keyar su zuwa gida sakamakon zargin su da aikata ayyukan assha.Abinda ya haifar da zanga-zanga a Taipei.

‘yan kasarTaiwan da yawan su ya kai 45 a mayar dasu kasar China a tsakanin ranakun littini da talata, kuma dukan su an tsare su ne a kasar Kenya a cikin shekarar 2014 da laifin aikata ayyukan kutse ta duniyar gizo wato INTERNET.

Kotu a kasar ta Kenya tayi watsi da karar su da aka shiga amma ta basu umurni da su bar kasar cikin sati ukku.

Wannan lamari ya bata wa Teipei rai domin ko ta zargi kasar China ne da sace wadannan ‘yan kasar nata kuma ta umurci Kenya data kaisu kasar ta.

Sai dai mai magana da yawun harkokin China da Taiwan din An Fengshan yace wadannan mutanen sun sace kudaden ‘yan kasar China da yawan su kai miliyoyi.

XS
SM
MD
LG