Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Siriya Sun Kwace Kauyuka 9 Da Goyon Bayan Dakarun Amurka


Amurka ta kuma kai hare-haren jirgin sama a Manbji cikin sa'o'i 24

Dakarun da ke samun goyon bayan Amurka sun kwace kauyuka wajen 9 a Siriya, wadanda ke daura da kan iyakar Turkiyya tun daga ranar Talata, a kokarinsu na dannawa zuwa garin Manbji da ke karkashin ikon ISIS.

Amurka ta kuma kai hare-haren jirgin sama a Manbji cikin sa'o'i 24 da su ka gabata, wadanda su ka yi sanadiyyar mutuwar farar hula wajen 15, uku daga ciki yara kanana, a cewar kungiyar kare hakkin dan adam a Siriya.

Majiyoyin soji da ke da nasaba da matakan soji da ake daukawa a Manbji sun gaya ma Muryar Amurka cewa mayakan ISIS na kwace iyalansu daga garin, amma kuma su na tilasta ma farar hulan garin su tsaya don su yi garkuwa da su. Sojojin sun ce an ceto kauyuka da dama ba tare da wata tirjiya kwakkwara daga ISIS ba.

Kungiyar Dakarun Jadda Dimokaradiyya A Siriya (SDF), wadda hadaka ce da Kurdawa ke jagoranta tare da taimakon wasu sojojin musamman na Amurka su 200, ta danna cikin yankunan da ke hannun mayakan na ISIS a bangare biyu na kogin Euphrabtes, abin da ya harzuka Larabawan Sunni da kuma Turkiyya, wadanda ke fargabar cewa Kurdawan na kokari ne su kafa nasu garin akan iyakar.

XS
SM
MD
LG