Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Saman Amurka Ne Ya Harba Makami Mai Linzamin


Mohamed Mohamud, wanda aka fi sani Dulyadeyn, shine kwamandan kungiyar 'yan bangan nan da ake jin tsoro ta "Amniyat" ta kungiyar al-Shabab,

Jami’an kasar Somaliyya sun ce mutumen da ya kittsa harin da aka kai a kan jami’ar Garissa a Kenya a shekarar da ta gabata ya mutu, wanada aka hallaka shi a wani samamen sojoji da tsakar daren jiya.

Mohamed Mohamud, wanda aka fi sani Dulyadeyn, shine kwamandan kungiyar 'yan bangan nan da ake jin tsoro ta "Amniyat" ta kungiyar al-Shabab, wacce kuma ake dorawa laifin kai mummunan harin nan da aka kai a watan Afrilun bara wanda ya hallaka mutane 148, galibinsu kuma dalibai ne.

Wani babban jami’in Somaliyya da ya so a sakaya sunansa ya fadi cewa jiragen saman Amurka masu saukar ungulu ne suka harba makami mai linzami, wanda ya auna motar da Dulyadyn ke ciki tare da wasu su 2.

Sai dai kuma ministan tsaro a yankin Jubba, Abdurashid Janan, ya fadawa muryar Amurka sashen Somaliyyanci cewa wasu dakarun Somaliyya -horon Amurka da ake kira Donab ne suka kashe dan bindigar.

An kai harin ne a kudancin garin Bula-Gaduud da ke kudancin Somaliyya, kusan kilomita 30 daga arewacin garin Kismayo.

XS
SM
MD
LG