Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 14,000 Ake Sa Ran Zasu Halarci Jana'izar Muhammad Ali


Muhammad Ali

Wannan hidimar jana'izar dai za'a yi ta a Louisville, jihar Kentucky

Mutane wajen 14,000 ake kyautata zaton za su taru don makokin rasuwar Muhammad Ali a wata jana'izar Musulunci, wadda za a yada ta kai tsaya ta gidajen talabijin da kuma kafafen sada zumunci.

Wannan hidimar jana'izar da za'a yi a Louisville, jahar Kentucky za'a yi ta ne a dandalin Freedom Hall, inda Ali ya fara wasan damban zamani na boxing a hukumance a 1960.

Musulmin Amurka da dama na duniya fatan cewa wannan hidimar jana'izar za ta nuna cewa an yi na'am da Musulunci a Amurka.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG