Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yarjejeniyar Tana Kasa Tana Dabo


Jiya aka ce gwamnatin Nigeria ta kula yarjejeniyar sulhu da kungiyar ‘yan yakin sa kan Niger Delta Avengers.

Tana yiwuwa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka kulla tsakanin gwamnatin Nigeria da kungiyar ‘yan yakin sa kan Niger Delta Avengers data yi ikirain kai hare haren da suka gurgunta harkar hakar mai a kasar, tana kasa tana dabo.

Jiya Talata wani jami’in NNPC ya fadawa Muryar Amirka cewa gwamnatin Nigeria ta kula yarjejeniyar sulhu da kungiyar ‘yan yakin sa kan Niger Delta Avengers.

To amma sai kungiyar ta Avengers ta maida martini a shafinta na twitter cewa bata kula wata yarjejeniya da gwamnatin Nigeria ba.

Hare haren da yan kungiyar Avengers suke kaiwa ya rage yawan man da Nigeria ke hakowa. A kwanan nan gwamnatin Nigeria ta bada sanarwar cewa zata rage yawan sojojin ta a yankin Niger Delta da kuma yi

shawarwarin samun zaman lafiya da kungiyar Avengers.

XS
SM
MD
LG