Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tasirin Zaben Britaniya Na Ficewa daga Tarayyar Turai Akan Siyasar Amurka


 'Yan takaran shugabancin Amurka, Trump na Republican da Clinton ta Democrats
'Yan takaran shugabancin Amurka, Trump na Republican da Clinton ta Democrats

Ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai ta shiga harkokin siyasar Amurka inda yadda 'yan takaran suka fuskanci lamarin zai yi tasiri akan goyon bayan jama'a da zasu samu ko su rasa

Ficewar da Britaniya tayi daga kunigyar Tarayyar Turai yana tada kura a fagen siyasar Amurka. Mutuminda ake sa ran jam'iyyar Republican zata tsaida takarar shugabancin Amurka Donald Trump yana kallon ficewar a zaman kara tabbatar da manufofinsa a wannan yakin neman zaben. Yayinda 'yar takarar shugabancin Amurka Hillary Clinton, ta kalli abunda ya faru a Ingila a kara zaman shaidar tabbatar da cewa Trump bai cancanci zama shugaban kasa ba.

Nasararar da masu neman ficewa daga kungiyar Tarayyar Turan suka samu, ta zowa gwamnatin Obama da-ba-zata, aka barta tana kame-kamen yadda zata bullowa lamarin ganin ba wannan ne sakamakon da taso ba.

Da yake magana kan sakamakon Donald Trump wanda yaje Scotland domin bude harkar kasuwancinsa ya goyi bayan sakamakon, yace jamaa'r kasar suna neman wani sabon 'yanci kusan za'a ce. Yace yana ganin danganataka tsakanin abunda ya faru a Britaniya da abunda yake faruwa a Amurka.

Kwamitin yakin neman zaben Mrs Clinton bai bata lokaci ba wajen amfani da kalaman Mr. Trump a wani sabon talla da yake nuna cewa duk wata fitin ko bala'i babu abunda Trump yake tunani illa ta yadda kurum zai sami riba.

Wata sabuwar kuri'ar neman jin ra'ayin jama'a ta nuna Mrs Clinton tana kan gaba da Trump da maki 12. Duk da haka masu zabe sun dage suna cewa suna son sabon alkibla.

XS
SM
MD
LG