Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Wasu Mutane Da Ake Zargi Da Hannu A Harin Istanbul


Jami’an Turkiyya sun zargi kungiyar ISIS a harin da aka kai

Yau Alhamis ‘yan sanda sun cafke wasu mutane 13 da ake zargi suna da hannu a hare haren da aka kai filin saukar jiragen sama dake Istanbul, wanda ya kashe mutane 42 da raunata wasu 239. A cewar kafar yada labarai ta Turkiyya.

An cafke mutanen ne a yayin wani hari da ‘yan sandan suka kai wasu gurare 16 a Instanbul. A kalla 3 daga cikin wadanda aka kama ba ‘yan Turkiyya bane.

A cewar kafar yada labarai mallakar gwamnatin Turkiyya, tace a birnin Izmir dake yammacin kasar jami’an sun kame wasu mutane 9 da ake zargin suna da alaka da mayakan IS ta hanyar taimaka musu da kudade da kuma nada sabbin mayaka.

Jami’an Turkiyya sun zargi kungiyar IS a harin da aka kai na filin saukar jiragen, duk da yake dai har yanzu babu wanda ya fito ya dauki alhakin harin.

A jiya Laraba dai Fara Minista Binali Yildirim, yace ana nan ana ci gaba da bincike kan harin, amma alamu na nuni ga kungiyar IS. Ya kuma yi tunanin an kai harin ne don mayar da martani kan yunkurin Turkiyya na inganta alakarta da kasar Rasha da Isra’ila.

3.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG